PSG ta yanke wa neymar farashi gami da tambayar da ake mata akan dan wasan.

Marca tace Neymar yana kokarin komawa Barcelona  ayayin da kulob din Paris saint German ta yanke mai farashin Euros miliyan 150 saboda suna tsammmanin zai bar kulob din su.
Darektan wasan kulob din Leonardo, ya yanke shawarar cewa zasu iya barin Neymar ya bar kulob din a karo na farko amma ba zasu taba barin Kylian Mbappe ya bar kulob din ba.
An samu labarin ne daga wajen dan jarida mai suna Julian Laurens na ESPN, euros miliyan 150 da PSG ta yanke wa neymar tayi kadan akan yadda yan Barcelona da lauyoyin Neymar suke tunani saboda sun buga FiFA shekarar data wuce kuma ya kai tsawon shekaru 3 a kulob din kuma ace basu Kara mai farashi ba.
Barcelona sun ci gaba da duba da wannan lamarin cewa, Abun mai mahimmance a gurin shugaban su Josep maria Barotmeu kuma Lionel Messi zai ji dadi da hakan.


© hutudole

Post a Comment

 
Top