Fitacciyar ‘yar wasan fina-finan Hausa, Maryam Booth, ta bayyana cewa bayan shawara da da ta yi da lauyoyin, ya zama dole ta maka Deezell a kotu.
Idan ba a manta ba, a makwannin da suka gabata aka saki wani bidiyon tsaraici na dake nuna jarymar tsirara a dakin Otel tana canja kaya.
Tun a wancan lokaci mutane da dama suka rika yin tir da wannan abu da suka ga wanda ya sami wannan bidiyon tsiraici na jarumar.
Ibrahim Rufai da aka fi sani da suna Deezell ne jarumar ta zarga cewa shine yake tare da ita a wannan daki kuma shine ya dauke da wayarsa.
Daga baya ya ce ba shi bane ya yada Bidiyon sannan kuma ya shigar da kara kotu bisa zargin kazafi da aka yi masa.
Bayan haka ne Maryam ta shifar da nata karar ta neman kotu ta tilata wa Deezell ya biya ta naira Miliyan 300 a dalilin tozarta ta da yayi na sakin wannan bidiyo.
Maryam ta ce ba tun yanzu ba Deezell ya rika yi mata barazanar yada wannan bidiyo yana neman ta bashi kudi ko ya yada.
” Ranar 27 ga watan Fabrairu a dakin Otel din Nanet dake Abuja ya dauki bidiyo batare da sanina ba.
” Na ce masa lallai ya goge wannan bidiyo.
” Amma ba tare da sanina ba sai ya yi kaman ya goge, ashe aika wa wani abokinsa yayi mai suna Ruky Haske
” Tun daga nan ya fara yi min barazanar sai ya sami bidiyon don ya bata ni ko kuma in ba shi kudo masu yawa.
Ta kara da cewa wannan abu da saka ta cikin dimuwa, takaici da damuwa maruka, Sannan ya shafi sana’ar ta.
Maryam ta nemi kitu tabi mata hakkin ta sannan kuma ta tilasta wa Deezell ya biya ta naira Miliyan 300 fiyyar abin da yayo mata.
Premiumtimeshausa
© hutudole
Post a Comment