A yau ne aka buga babban wasan hamayya a gasar Premier league ta kasar Ingila wanda ya faru tsakanin manyan kungiyoyin gasar, Manchester United da Manchester City inda City ta sha kashi da ci 2-0.

Martial ne ya fara ciwa United kwallo ana mintuna 30 da fara wasa, sai kuma Scott Mctominay da ya ci kwallo ta 2 bayan karin lokaci ana gab da za’a tashi, kuskuren golan Manchester City, Ederson ne ya jawo mata kwallon ta biyu inda maimakon ya baiwa dan garinsu kwallon sai ya baiwa Mactominay.

An sako dan kwallon Najeriya me bugawa kungiyar wasa,Odion Ighalo ana mintuna kadan a tashi. Wannanne babban wasansa na farko a kungiyar a gasar Premier kuma ga dukkan alamu ya ji dadin buga wasa ya kuma yi rawar gani. Tun bayan komawarshi kungiyar har yanzu Manchester United ba ta yi rashin nasara ba.

Aaron Wanbissaka yayi rawar gani sosai a wasan inda yayi tare da kuma nuna bajinta ta gani ta fada

Mahrez ma ya haskaka a wasan duk da cewa Manchester City basu yi nasara ba amma abinda yawa Branden Williams ya dauki hankula sosai:

 

Kalla a kasa:

Kalli maimacin bajintar da yayi a wasan na yau a kasa inda ya hana Sterling sakat.

 



© hutudole

Post a Comment

 
Top