Tun bayan sauke Muhamma Sanusi II da gwamnatin jihar Kano ta yi daga sarkin Kano, sai ya fara samun sabbin mukamai daga wajen jihar.
Lamarin sauke sarki Sanusi II ya dauki hankula sosai a ciki da wajen kasarnan.
Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, CBN yanzu haka ya samu mukamai guda 3 kamar haka:
Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai wanda abokine ga sarki Sanusi II tun suna yara shine na farko da ya fara baiwa Sarki Sanusi mukami.
Ya bashi mukamin mataimakin kwamitin hukumar kula da zuba jari a jihar Kaduna watau KADIPA.
Sannan kuma ya bashi shugaban jami’ar jihar ta Kaduna watau KASU.
Itama jihar Ekiti ta bayyyana cewa zata ci gaba da rike Sarki Sanusi II a matsayin shugaban jami’ar jihar duk da saukeshi da Sarautar da aka yi.
© hutudole
Post a Comment