A yayin da Duniya ke ci gaba da yakar cutar Coronavirus/COVID-19 Najeriya ma na iya nata kokarin dan ganin ta kare al’ummarta daga Annobar dake neman durkusar da al’amuran Duniya.

 

A jiya, Asabarne aka samu karin mutane 10 dake dauke da cutar, 7 a Legas,sannan a karin farko aka samu 3 a Abuja. Hakan ya kai yawan wanda aka samu da cutar a Najeriya zuwa 22. Kuma hukumar Lafiya ta kasa ta bayyana cewa dukansu 10 ‘yan Najeriya ne da suka yi tafiye-tafiye zuwa kasashen waje a makon da ya gabata.

 

An sallami dan kasar Italiyarnan da ya fara shigowa da cutar Najeriya bayan da ya warke.

 

Najeriya ta kulle filayen jiragen samanta kaf ga jiragen kasashen waje in banda na laruri, hakan zai fara aikine nan da Gobe, Litinin 23 ga watan Maris. Saidai jiragen cikin gida zasu ci gaba da jigilar kamar yanda aka saba.

 

Hakanan hukumar kula da jigilar jiragen kasa NRC ta bayyana cewa daga Gobe, Litinin, 23 ga watan Maris itama zata dakatar da jigilar a kasa baki daya dan hana yaduwar cutar.

 

Saidai daga baya hukumar ta jigila ta jirgin kasa ta bayyana cewa, kamin ta dauki mutane sai sun bada cikakken sunansu da ranakun haihuwarsa da inda suka fito da kuma inda zasu, hukumar ta bukaci fasinjoji da su bayar da hadin kai dan ganin an kare yaduwar cutar ta Coronavirus.

 

Shugaban hukumar lafiya ta kasashe renon kasar Ingila, Dr. Osaho Enabulele ya bayyana cewa laifin gwamnatin tarayya ne yaduwar cutar haka. Yace tun da farko da aka ga alamun cutar ya kamata ace an rufe iyakokin Najeriya ba wai yanzu da ta shigo kasar gadan-gadan ba.

 

Yace kasashen Africa irinsu Uganda sun dauki irin wadannan matakai na gaggawar rufe iyakokinsu da wuri kuma gashi cutar bata musu yabmwa ba tunda dai ansan cewa daga kasashen waje ake kawota.

 

Yayi wannan korafine yayin da ya kai ziyara Asibitin koyarwa na jami’ar Abuja inda ya kuma bayyana cewa kayan aikin da aka ware dan kula da cutar sun yi kadan, ya kamata gwamnati ta kara kaimi.

 

Itama dai jam’iyyar Adawa ta PDP ta bakin shugabanta, Uche Secondus ta dora alhakin yaduwar cutar a Najeriya kan shugaban kasa, Muhamadu Buhari inda a hirarsa da Punch yace, abinda ke faruwa kenan idan aka samu shugaban da bai san aikinsa ba, tun tuni ya kamata a rufe iyakokin Najeriya amma sai yanzu da cutar ta shigo karara, gashi yanzu ba’a san iya yawan wanda suka yi ma’a mala da masu dauke da cutar ba sannan kuma ina da ina suka shiga.

 

Secondus ya baiwa ‘yan Najeriya shawarar kula da tsafta dan hakanne zai rage yaduwar cutar.

 

Tuni coci-coci a Najeriya suka fara gudanar da Ibadunsu ta hanyar Yanar gizo bayan da aka hana taruwa da yawa a yi Ibada.

 

Masana ilimin lafiya dai na bada shawarar wanke hannu akai-akai, kiyaye taba ido da kwakular hanci da gaisuwa da shiga taro me yawa.

 

 

 

 



© hutudole

Post a Comment

 
Top