Tawagar Liverpool ce ta fi ko wacce tsada a kasuwar musayen ‘yan wasa tsakanin manyan Gasannin Turai biyar, kamar yadda binciken kungiyar CIES da ke bibiyar kwallon kafa ya bayyana.

 

Liverpool ta haura takwararta ta Premier Manchester City da yawan kudin da suka kai yuro biliyan 1.4, wanda suka yi daidai da fam biliyan 1.27, yayin da Man City take da fam biliyan 1.24, kuma take matsayi na biyu a jerin.

 

Chelsea ce ta biyar a jadawalin, yayin da Manchester United da Tottenham ke cikin jerin kungiyoyi goman farko.

 

Da jumlar darajar kudi da suka kai fam miliyan 33.7 kungiyoyin Bundesliga su ne a karshen jadawalin.

 

Liverpool da ke jan ragamar Gasar Premier na bukatar cin wasa biyu ne kawai cikin wasa taran da ya yi ragowa a gasar domin ta lashe ta, karo na farko kenan cikin shekara 30.

 

Ta lashe Gasar Zakarun Turai a bara ta kuma kara da kofin Uefa Super Cup tare da kofin zakarun nahiyoyi duk a lokaci guda.

 

Frank Lampard ne ke matsayi na biyar a jadawalin, inda tawagarsa ta kai darajar kudi fam miliyan 917.

 

Sai dai CIES ta ce darajarta ta kara dagawa sakamakon barkewar annobar da ta shafi da yawa daga cikin matasan ‘yan kwallonta, da kuma hana mata damar sayen ‘yan wasa da Fifa ta yi.

 

CIES ta yi amfani da ma’aunai daban-daban wajen fitar da darajar kungiyoyin, wadanda suka hada da shekarun ‘yan kwallo da kokarinsu da tattalin arzikin kungiyar da dai sauransu.

 

Kylian Mbappe na Paris St-Germain mai shekara 21, shi ne ya fi ko wanne dan wasa daraja wanda ya haura fam miliyan 227.

 

Jadawalin kungiyoyin da suka fi daraja a Duniya.

 

Club Country Value (m/euros)
Liverpool England 1,405
Manchester City England 1,361
Barcelona Spain 1,170
Real Madrid Spain 1,100
Chelsea England 1,008
Manchester United England 1,007
Paris St-Germain France 979
Atletico Madrid Spain 836
Tottenham England 787
Juventus Italy 783

 

BBChausa.



© hutudole

Post a Comment

 
Top