Tsohowa mai kimanin shekaru 103 yar asalin kasar Iran ta warke daga cutar corona.

Tsohuwar dai an bayyana ita ce mafi tsofa da takamu da cutar covid19 kuma ta samu sauki cikin sati daya.

Duk kuwa da yawan shekaru da wannan tsohuwa ke dashi kuma bincike ya tabbatar da masu yawan shekaru sunfi hatsarin kamuwa da wannan cuta, amma sai gashi wannan tsohuwa wanda ba’a bayyana sunan taba ta kamu da wannan cuta kuma ta warke garau abinta.

Tun dafarko dai an kwantar da tsohuwar ne a wani asibiti dake cikin birnin Semnan har tsawan sati kamar yadda IRN ta rawaito, an kuma sallameta ne bayan data warke daga cutar.

An kuma bayyana da cewa tsohuwar ita ce ta biyu mai yawan shekaru data kamu da cutar Corona a kasar Iran wadda kuma ta samu sauki, a kwai wani dadtijo mai kimanin shekaru 91 mai suna Kerman wanda shema ya kamu da cutar Kerman ya kasance ma zaunine a kudu maso gabas dake kasar Iran kamar yadda kamfanin dallancin labarai suka bayyana.

Dadtijon ya fara jin alamomin cutar ne har tsawan kwana uku inda bayan an Kai shi asibiti a ranar litinin likitoci suka tabbatar da samun saukin shi duk kuwa da cewa yana fama da hawan jini da kuma asthma.

Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta bayyana adadin wanda cutar tai sanadin mutuwar su a wannan wata ya kai kusan 3.2 wanda adadin wanda suka kai shekara 80 ya kai 21.9.



© Abubakar Saddiq

Post a Comment

 
Top