Dan kwallon Bayern Munich, Robert Lewandowski da matarsa Anna sun bayar da gudunmuwar Euro miliyan daya domin yaki da cutar coronavirus.

 

 

Sauran ‘yan wasan Munich Leon Goretzka da Joshua Kimmich sun kafa gidauniya mai suna We Kick Corona domin yaki da annobar, kuma a tsakaninsu sun bayar da gudunmuwar Euro miliyan daya.

 

 

Shi ma dan kwallon Manchester City, Leroy Sane ya bayar da kyautar kudi don yakar cutar.

 

 

“Muna cikin yanayi maras dadi,” in ji Lewandowski.

 

 

Kawo yanzu gidauniyar We Kick Corona ta tara fiye da Euro miliyan biyu da rabi.

BBChausa.



© hutudole

Post a Comment

 
Top