Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana abinda ya gani a sansanin ‘yan gudun hijira wadda ‘yan Boko Haram suka fatattaka a yanzu.

 

Shugaba Buhari, ya ce ya ga abubuwan tashin hankali da alhini, saboda haka ne ya sa ba zai iya komawa can ba, Buhari ya ce, ya ga yara kanana da basu san iyayensu ba balle su san daga inda suka fito.

 

“Na je sansani uku kacal amma tun daga nan ban iya komawa ba saboda ba zan iya jure ganin halin da suke ciki ba,”.

 

“Abinda na gani a sansanin ‘yan gudun hijira ya firgita ni matuka.

 

Ina son yin tsokaci a kan ziyarar da na kai sansanin ‘yan gudun hijira.

 

Gaskiya mummunan lamarin da na gani ne yasa na bukaci daya daga cikin manyan sojojin da muke dashi a kasar, Janar T.Y Danjuma a kan ya shugabanci ma’aikatar.

 

“Saboda abinda muke samu daga kungiyoyin taimakon kai da kai baya zuwa inda ya dace kuma”.



© hutudole

Post a Comment

 
Top