Hukumar koli ta addinin Musulunci a Jamhuriyar Nijar ta sanar da soke tarukan sallar juma’a da sauran sallolin jam’i bayan hukumomi sun bayyana samun mutum na farko da cutar coronavirus ta kama a kasar.
Haka zalika, su ma jagororin addinin kirista sun bukaci mabiyansu su dakatar da tarukan ibada a coci-coci musamman ma dai na karshen mako.
Wannan ne karon farko da cutar coronavirus ta bulla a Nijar tun bayan barkewarta a duniya karshen watan Disamba, kwanaki kalilan bayan hukumomin kasar sun sanar da rufe iyakokinsu don hana bazuwarta.
Tun da farko, ministan lafiya na Nijar Dakta Idi Iliyasou Mainasara ya shaida wa BBC cewa mutumin da ya kamu da cutar dan kasar ne mai shekara 36.
“Yana aiki a wani kamfanin zirga-zirgar motoci, bayan ya fito daga Lome, ya je Ghana ya je Burkina Faso, sannan ya dawo Jamhuriyar Nijar,” in ji ministan.
“Bayan ‘yan kwanaki kadan da gano alamomin wannan ciwon, a lokacin ne aka shiga yi masa bincike sannan da aka gano yana da cutar (don haka) sai aka kwantar da shi”.
Yanzu haka yana wani wuri da gwamnati ta yi tanadi kuma ana yi masa magani, maganin kuma ga alama ya karbe shi, don haka yana nan ana ta yi masa kuma akwai sauki a maganin da ake masa, kamar yadda ministan ya fada.
A cewarsa tuni aka killace iyalin maras lafiyan su ma kuma matakin killacewar abu ne da gwamnatin kasar ta dauka a baya-bayan nan ga mutanen da suka shiga kasar daga wasu kasashe.
© hutudole
Post a Comment