Tauraron dan kwallon Brazil da Barcelona, Ronaldinho dake tsare a gidan Maza na kasar Paraguay na cikin annashuwa dan kuwa har ya buga kwallo kuma yayi nasara.

 

Hukumomin kasar Paraguay sun kama Ronaldinho inda suka daureshi a gidan yari shi da dan uwansa bayan kamasu da laifin shiga kasar da takardun bizar Bogi.

 

Saidai lauyan dan wasan me shekaru 39 ya bayyana cewa Ronaldinho bai san cewa fasfon bogine aka bashi ba, yace ya kamata ace hukumar kasar ta lura da wannan abu.

 

An bada belin Ronaldinho akan Yuro Miliyan 4 saidai har yanzu yana tsare dan babu wanda yayi belin nasa.

 

An ruwaito cewa tsohon abokin wasansa, Messi yayi yunkurin ceto dan wasan saidai na kusa da Messin sun karyata wannan zargi inda suka ce Messi baiji dadin abinda ya faru da Ronaldinho ba amma bai yi yunkurin biyan kudin belinsa ba hakanan kuma bai ce zai aika lauyoyi su kareshi ba.

Ronaldinho mutum ne me fara’a sosai dan kuwa koda a fili idan yana buga kwallo zaka ga an bugeshi ya fadi amma haka zai tashi yana murmushi. A yayin da yake zaman gidan yari, wani ma’aikacin gidan yarin ya gayawa Reuters cewa Ronaldinho ya kasance cikin murmushi kamar yanda aka sanshi a waje.

 

Ya shiga wata gasar kwallon kafa da ake bugawa a gidan yarin inda ya ci kwallaye 5 ya kuma bayar da taimako aka ci guda 6, an tashi wasan bangren Ronaldinho yayi nasara da sakamakon 11-2.

 

Ronaldinho ya lashe kyautar Ballon d’Or,ya ci kofin Champions League da Kofin Duniya dana La lagi dadai sauransu kuma gwani na gwanayene a harkar kwallo wanda indai zaka kalleshi to zai nishadantar dakai.



© hutudole

Post a Comment

 
Top