Masu iya magana kance garin kwadai kuda ke mutuwa. Sannan wanda bai ji bari ba, ya ji hoho. Kusan hakane ta faru da wani magidanci da ya ci amanar matarsa da karuwarsa.

 

Magidancin dan kasar Ingila, ya je kasar Italiyane inda ya hadu da karuwar tasa, saidai yayi sa’a inda ya koma gida Ingila kamin a rufe iyakar kasar ta Italiya.

 

Sanadiyyar lalatar da yayi da Karuwar tasa a Italiya, Ashe ya dauko muguwar cutarnan data addabi Duniya watau Coronavirus/COVID-19.

 

Tuni dai aka killaceshi shi da matarshi kamar yanda Rahoton the Sun ta kasar ta ruwaito.

 

Saidai ya gayawa Likitoci ta yanda ya samu cutar amma yaki ya fadi sunan karuwar tasa data goga mai cutar.

 

Ya hakikance cewa ko me za’a mai ba zai taba bayyana sunan karuwar tasa ba.

 

Kasar Italiya dai itace kasar Turai data fi kowacce yawan masu cutar inda a yanzu suka haura 2000

 



© hutudole

Post a Comment

 
Top