Shugaban jam’iyyar APC,  Adams Oshiomhole ya gabatarwa da shugaban kasa, Muhammad Buhari da Sabon mataimakinshi, Tsohon gwamnan jihar Oyo, Sirikin Gwamnan Kano,Sanata Abiola Ajimobi.

 

Oshiomhole ya bayyanawa manema labarai hakane bayan ganawar da suka yi da shugaban kasar a jiya,Juma’a. Ya bayyana cewa dama yankin Yarbawane zasu kawo mataimakin shugaban jam’iyya kuma sun gabatar da Ajimobi duk da cewa jihar Ekiti bata goyon bayan hakan amma an fita yawa.

 

Oshiomhole ya kuma yabawa shugaba Buhari kan kokarin da yake wajan ganin an dakile yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19 a Najeriya.

 

 



© hutudole

Post a Comment

 
Top