Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta baiwa gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai shawarar cewa tunda dai yana son tsohon sarkin Kano,Muhammad Sanusi II haka to abinda zai yi shine kawai ya bude sabuwar masarauta a Kaduna sai yawa Sanusi II sabon nadin Sarauta.
APC jihar Kano har ta baiwa El-Rufai shawarar daga inda zai fitar da sabuwar masarautar da kuma sunan da zai bata.
Hakan na kunshene a cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Kano, Alhaji Shehu Maigari ya sakawa hannu, kamar yanda Daily Trust ta ruwaito.
Sanarwar na cewa” Ranka ya dade gwamna Nasiru El-Rufai wannan fa mutum ne da yake yiwa jam’iyyarka ta APC zagon kasa ya kuma caccaki shugaban kasa, Muhammadu Buhari, mutumin da kake kallo a matsayin abin koyinka, ba tare da yana da wata hujja ba amma gashi kana ta mai abubuwan karramawa kamar wani gwarzo.
Sanarwar ta ci gaba da cewa,”Ranka ya dade, APC jihar Kano na baka shawara da babbar murya cewa ka bude sabuwar masarauta a Kaduna wadda zaka sawa suna sabuwar majalisar Sarakunan Kaduna. Zaka iya yin wannan masarauta daga Rigachukun zuwa Kasuwar Magani. Kaga sai ka saka gwarzonka ya zama sarki dan ya ci gaba da yiwa jam’iyyarshi ta PDP aiki. Bawai wadannan mukamai da ka bashi na wucin gadi ba.
Gwamnan Kaduna ya baiwa Tsohon Sarki,Muhammad Sanusi II mukamai har biyu bayan da gwamnatin Kano ta tsigeshi daga sarauta. Mukaman sune shugaban jami’ar Kaduna,KASU da kuma mataimakin shugaban hukukmar kula da zuba jari ta jihar ta Kaduna, KADIPA
© hutudole
Post a Comment