Tsohon sarkin Kano,Muhammad Sanusi II ya bayana cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba wajan ganin an samu daidaito tsakanin mata da maza a wajan ayyukan ci gaban kasa ba.

 

Sanusi II yayi wannan maganane a wajan wani taro da aka gudanar kan samun daidaito tsakanin jinsi da kuma dena tauyewa mata hakkinsu a Abuja kamar yanda Vanguard ta ruwaito.

 

Yace zai ci gaba da yakar Al’adar aurar da mata ‘yan kasa da shekaru 18.

 

Yace ba’a cika saka mata cikin harkokin ayyukan ci gaban kasa ba a Najeriya. Dan haka yana kira ga masu rike da madafan Iko da su rika kula mata wajan ayyukan ci gaba.

 

Yace mata suna da muhimmiyar rawa da suke takawa a ci gaban rayuwar Alumma dan sune ginshikin bayan ci gaban kasa saboda hakan na ta’allakane kan yanda suka baiwa ‘ya’yansu tarbiyya.

 

Yace bisa al’ada muna girmama iyayenmu mata. Dan haka ina kira ga kowa da kowa mu ci gaba da baiwa mata muhimmanci musamman a farkon rayuwarsu.

 

Yace dolene mu ci gaba da yakar al-adar dake hana ruwa gudu wajan cimma daidaito tsakanin jinsi. Ya kara da cewa zan ci gaba da yakar al’adar aurar da mata ‘yan kasa da shekaru 18

 



© hutudole

Post a Comment

 
Top