Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, ya nisanta kansa kan labarin karya da ake yadawa, wai ya nada ‘yar wasan Hausa, Maryam Aliyu Obaje, wadda aka fi sani da Madam Korede mukamin babbar mataimakiyar sa ta musamman kan harkokin sadarwar zamani.

 

A bayanin da mai baiwa gwamna shawara akan hakokin yada labarai Muhammad Bello, ya bayya nawa manema labarai, kuma ya yi kira ga jama’a su daina daukar maganan da ake yadawa a kafafen sada zumunta don ba gaskiya ba ne.

 

A cewar gwamna wanda a halin yanzu yana jihar Delta ya tabbatar da cewa bai batar da irin wannan mukamin a gwamnatin sa ba.



© hutudole

Post a Comment

 
Top