A jiya ne gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce abin takaici ne yadda sannu a hankali shugabancin hukumar Hisbah yake kaucewa daga kan turbarsa ta ainahi.

Gwamnan ya fadi hakan a sa'ilin da yake jawabi a gurin taron daurin auren mata 70 cikin 1,500 da gwamnatinsa ta aurar, wanda aka gabatar a babban Masallacin Kano.

Ya ce: "Gwamnati ba za ta kuma zuba ido a kan kura-kuran da shugabancin Hisbah ya ke ba. Shugabancin da ya kyautu ya bi dokokin Kur'ani da Hadisin Annabi Muhammad (SAW), na bin ra'ayin wasu mutane.

"Sannan abin kaico, saboda jahilcin shugabannin Hisbah, sun yi imanin yabon mutane abin kirki ne. Wannan ba mai yuwuwa ba ne, kuma dole gwamnati ta magance wannan matsalar."
Sarauniya.

Post a Comment

 
Top