Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da hana manyan gangami da tarukka a fadin jihar.
Hatta salloli a masallatai da tarukkan bauta a Coci-coci duk an hana.
A takarda da gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya fitar, da Kakakin sa Muyiwa Adekeye ya aaka wa hannu gwamnati ta yi haka ne don kare mutanen jihar daga kamuwa da Coronavirus.
Ga dokokin
1 – Gwamnatin Kaduna ta umarci duk masallan Kaduna su dakatar da yin sallolin jam’in a masallatai. A rika Yi a gida saboda a dakile yaduwar cutar.
2 – Kiristoci su dakatar da tarukka ibada a Coci-coci daga yanzu. Idan ya kama, kada a wuce mutane 10 a lokaci daya.
3 – Duk wani gangami a garin Kaduna da ya wuce mutane 50 ya haramta daga yanzu.
4 – Gwamnati ta rufe makarantun jihar, tun daga Firamare zuwa sakandare da manyan makarantu.
5 – Gwamnati ta hana taron Holewa, Disko, mashaya, wuraren Kallo, tarukka da sauran su.
Idan ba a manta ba a ranar Alhamis ne Sakataren ma’aikatar Ilimi, Sunny Echono ya bayyana cewa gwamnati ta umarci duka makarantu a kasar nan, Kama daga Jami’o’i ne, Kwalejojin Ilimi, makarantun Sakandare, Makarantun Firamare duk su rufe makarantun har sai lokacin da gwamnati ta ce a dawo.
Dama Kuma Idan ba a manta ba gwamnonin yankin Arewa Maso Yamma sun sanar da rufe duka makarantun yankin saboda cutar coronavirus.
Har yanzu dai ba a tabbatar da kamuwan ko da mutum daya ne a yankin Arewa da Kudu masu Gabashin Najeriya.
Premiumtimeshausa
© hutudole
Post a Comment