An dakatar da gaba daya manyan gasannin lig na kwallon kafa a kasashen nahiyar Turai a makon da ya gabata, a wani al’amari da ya jefa wasan kwallon kafa a cikin wani kalubalen da bai taba fuskanta ba a wannan zamani, kuma bisa ga dukkan alamu, dole ne ma a dau mataki a kan gasannin zakarun nahiyar Turai, wato Champions League da Europa League.

Hukumar kwallon kafar Turai a yau Talata za ta gudanar da wani taro na wakilai 55 na hukumomin kwallon kafa na kasashe da kungiyoyi, sannan daga bisani ta gudanar da taron majalisar zartaswarta a shelkwatarta da ke Switzerland.

Nahiyar Turai ta kasance tamkar cibiyar wannan annoba ta coronavirus, inda yanzu haka hukumomi suka garkame kofofi a Italiya da Spain, yayin da Faransa ke biye, haka kuma sauran kasashe a nahiyar suke garkame iyakoki don dakile yaduwar wannan cuta.

Fiye da mutane dubu 2 da dari 1 ne suka mutu a Italiya, kasar da za ta karbi bakoncin wasan farko na wannan gasa ta Euro 2020.



© Abubakar Saddiq

Post a Comment

 
Top