A Najeriya shugabanin Kungiyoyi sun kalubalanci Majalisar dokokin Kasar da ta gaggauta yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya gyara ta yadda zai hana gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi cire Sarki mai daraja ta daya.

 

A wata zantawa ta musamman da Muryar Amurka ta yi da shugabanin wasu kungiyoyi a Abuja, sun yi la’akari da yawan maganganun da suka taso ne a game da cire tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu, inda suka nuna yatsa ga Gwamnoni da ma ‘yan siyasa akan cewa su ne suke wulakanta masarautun gargajiya tare da rage masu kima da karfi a cikin a’lummarsu, ta hanyar jawo su cikin harkokin siyasa da kuma koya masu kwadayi.

 

Shugaban wata kungiya mai zaman kanta da ake kira Save The Change, Alhaji Bashir Danmusa, ya yi kira ga kwamitin da majalisar dattawan Najeriya ta nada domin ya yi wa kundin tsarin mulkin kasa garambawul da ya hanzarta yin gyaran ta hanyar yin dokar da zata hana gwamnoni ko majalisun jihohi cire Sarki mai daraja ta daya ba tare da amincewar majalisar dokokin kasa ba. A cewar sa, akan laifin da bai taka kara ya karya ba, sai a cire sarki haka kawai babu tuhuma babu jan kunne. Danmusa ya kuma ce siyasa ce ta shiga ta dagula al’amuran baki daya.

 

Shi ma Shugaban kungiyar habbaka Matasan Arewa Maso Gabas Alhaji Abdurahman Kwacham, ya ce cire sarki Mohammadu Sanusi na biyu ya zama abin kunya, kuma ya zubar wa kasar da mutunci a idanun duniya. Kwacham ya ce Sarkin mai ilimi ne kuma kwararre a harkar diflomasiyar kasa-da-kasa, saboda haka yana kira da a yi maza a hana aukuwar irin wanan mataki ta hanyar yin doka da sa ido akan gwamnoni da majalisun jihohi da ma ‘yan siyasa baki daya.

 

Daya daga cikin ‘yan asalin jihar Kano mazaunin birnin Abuja, Ado Sumaila, ya ce an riga an gurbata masarautun Kano gaba daya, saboda haka a yi maza-maza a yi wa tukkar hanci saboda a hana ci gaban irin wanan mataki.

 

Amma ga tsohon Ministan Wasanni da Matasa Barista Solomon Dalung, ya ce cire sarkin ya tona asirin Arewa ne, saboda ‘yan arewa na da riko. Dalung ya ce a yanzu haka Arewa ba ta da alkibla domin ba ta bin dokokin addinanta gaba daya.

 

A shekarar 1930 ne turawan mulkin mallaka suka kirkiri dokar fitar da sarakuna daga garuruwansu idan har an samu nasarar kwabe masu rawani.



© hutudole

Post a Comment

 
Top