Dan wasa Pierre Emerick Aubameyang mai taka leda a kungiyarsa ta Arsernal kuma kyaftin din kungiyar.

Kungiyarsa ta kwallan kafa ta Arsenal ta sanya wa dan wasan wanda kungiyar Barcelona ke zawarci, farashin fam miliyan hamsin.

Rahotanni sun ce Arsenal ta fadawa Barcelona cewa dole ne su biya fam miliyan 50 idan har suna son sayen kyaftin din kungiyar Aubameyang a wannan kakakar wasan.

Aubameyang dai na da ragowar watanni 18 kacal ne a kunshin kwantiraginsa da Arsenal kuma har zuwa yanzu ya ki amincewa ya sabunta kwantiragin nasa da Arsenal din.

Aubameyang mai shekaru 30 da haihua kuma dan asalin kasar Gabon, ya dawo kungiyar Arsenal ne a shekarar 2018 daga kungiyar Borussia Dortmond, akan farashin fam milyan hamsin da bakwai, farashin da ya ke shi ne kudi mafi yawa da Arsenal ta sa ta sayi dan wasa.

Zuwa yanzu dai Aubameyang ya zurawa Arsenal kwallaye 61 a adadin wasanni 97 a gasa daban-daban.

Barcelona ta so sayen Aubameyang a watan Janairu biyo bayan rauni da Suarez ya samu, amma sai ciniki bai fada ba.

Barcelona za ta sake mika tayinta a karshen kakar bana don daukar Aubameyang din, kuma shi ma dan wasan na son zuwa Barcelonan



© Abubakar Saddiq

Post a Comment

 
Top