Gwamnatin tarayya ta sanar da dakatar da daukar sabbin ma’aikata da maye gurbin ma’aikata har sai nan da zuwa wani lokaci idan al’amura suka daidaita.
Ministan kudi da tsare-tsaren kasa,Zainab Ahmad ce ta bayyanawa manema labarai haka a babban birnin tarayyan Abuja bayan kammala taron majalisar zartaswa na Ranar Laraba.
Saidai tace gwanati zata ci gaba da biyan Albashi da kuma biyan kudin fansho kamar yanda shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya bayar da umarni. Dan haka babu maganar rage ma’aikata.
Zainab ta bayyana cewa gwamnati ta dauki wannan matakine saboda matsalar tattalin arziki da Cutar Coronavirus/COVID-19 ta kawowa Najeriya.
Tace a yanzu haka Albasin da ake biyan ma’aikata kudin yayi yawa. Dan haka an dakatar da daukar sabbin ma’aikata har yanda hali yayi. Amma nan gaba idan lamura suka daidaita za’a ci gaba.
© hutudole
Post a Comment