Amurka ta yi gwajin wani sabon makami mai linzami da aka yi wa lakabi da ‘Hypersonic Missile’ wanda ke iya mamaye makaman abokan gaba duk inda suke kuma ya hana su tasiri.

 

Ma’aikatar Tsaron kasar ta ce,  makamin da aka gwada ya yi tafiyar da ya zarce sauti har sau biyar domin cimma inda aka ba shi umurni.

 

Vice Admiral Johnny Wolfe ya ce, sun samu nasarar wannan gwajin kuma yanzu za su mayar da hankalinsu a mataki na gaba wajen kara masa karfi fiye da yadda yake yanzu.

 

Makamin Hypersonic zai daga kimar yaki da makamai masu linzami zuwa wani matakin fargaba saboda tsananin gudun da suke da shi da ya zarce na makaman nukiliya da ake da shi yanzu haka, kuma ana iya sauya alkiblarsa a koda yaushe domin ganin ba a samu nasara a kan su ba.

 

A watan Disamban bara, kasar Rasha ta sanar da kaddamar da nata makamin na Hypersonic da aka yi wa suna Avangard, inda ta zama kasar duniya ta farko da ta sanar da amfani da shi.

 

Jami’an kasar sun sanar cewa, sabon makamin na tafiyar akalla kilimota 33,000 cikin sa’a guda.

 

Ita ma kasar China ta zuba jari sosai wajen gina nata makamin da ta kira DF-17 ‘Hypersonic Glide’ wanda aka gabatar wajen faretin sojin ranar ‘yancin kasar.



© hutudole

Post a Comment

 
Top