Kungiyar iyayen dalibai ‘yan asalin jihar Kano dake karantar likitanci a kasar Sudan ta nemi gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje kan ya taimaka musu wajen dawowa da daliban Kano gida daga kasar Sudan.
Shugaban kungiyar iyayen daliban Ahmad Baffa Usman ya bayyana cewa, tuni gwamnatin kasar Sudan ta bada sanarwar rufe jami’o’in kasar gabaki daya saboda cutar ta Coronavirus.
Wanda hakan ya sanya, hukumomin makarantun da dalibai ‘yan jihar Kano suke, suka baya da hutun wata uku, duba da karatowar watan azumi.
Rufe makarantun ya sanya daliban cikin wani hali, a don haka suke neman gwamnan Kano kan ya karasa ladan sa, ya dawo da daliban gida.
Wakilin mu Nasir Salisu Zango ya tuntubi shugaban hukumar bada tallafin karatu ta jihar Kano, Zakari Habu P.A wanda ya ce gwamnatin Kano za tayi iya kokarin ta wajen ganin an share hawayen wadannan daliban.
Freedomradio
© hutudole
Post a Comment