Tsohon kocin Arsenal, Arsene Wenger ya bayyana cewa duk da matsalar Coronavirus/COVID-19 da ake fama da ita a Duniya akwai bukatar a kamala gasar Premier League.

 

Wenger ya bayyana hakane a hirar da yai da TalkSport inda yace yasan Premier League na son kammala wasanninta na kakar wasan bana.

 

Yace za’aikata matsar da jadawalin buga wasannin har zuwa watan Yuni.

 

Shia dai Wenger na can kebe a kasarshi ta Faransa.

 



© hutudole

Post a Comment

 
Top