Hukumomin Najeriya sun dakatar da ayyukan matsugunin da ake ajiye matasa masu hidimar kasa dan basu Horo na kwanaki 21 kamin aikasu inda zasu yi aikin hidimar kasar.

 

Ranar 10 ga watan Maris ne matasan suka shiga wadannan matsugunai dake fadin kasarnan inda ake tsammin cewa zasu kwashe kwanaki 21 a ciki.

 

To saidai kwatsam cikin dare wajan karfe 1 sai aka bayyanawa matasan cewa za’a rufe matsugunan kuma aka fara basu takardun inda zasu je su fara aikin hidimtawa kasar.

 

Wasu dake cikin irin wadannan matsugunai sun tabbatarwa da Premium times da lamarin inda sukace an basu takardun zuwa inda zasu fara aikin hidimtawa kasa a jihohin Gombe da Plateau.

 

Wasu dake matsugunin jihar Delta sun tabbatarwa da shafin hutudole cewa an basu umarnin barin matsugunan inda aka raba musu da takardun zuwa inda zasu fara aikin bautar kasar.

 

Wannan na zuwane bayan da gwamnatin tarayya ta yanke shawarar cewa a dakatar da duk wasu taron jama’a da kuma hana jami’an gwamnatin tarayya tafiye-tafiye.



© hutudole

Post a Comment

 
Top