‘Yansanda a jihar Legas sun kama wani karamin yaro me shekaru 14 da laifin yiwa wasu yara maza 2 masu kimanin shekaru 7 da 5 fyade.

 

Lamarin ya farune a yankin Alimosho inda aka kama yaron yayin da yake tsaka da aika-aikar.

 

PMexpress ta bayyana yansanda tuni suka kama yaron tare kaishi gaban kotu inda kotun ta bukaci a ajiyeshi a gidan maza har zuwa 7 ga watan Aprilu da za’a ci gana da shari’ar.



© hutudole

Post a Comment

 
Top