Shugaban Majalisar shura na malamai na kasa , na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnsh (JIBWIS), Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya yi kira ga gwamnatocin tarayya da na jihohi da kar su hana yin sallar jam’i a Masallatai.
Shehun malamin yayi wannan kiranne a ranar juma’a a garin jos, inda ya bayyana da cewa Cutar corona yakin tattalin arziki ne tsakanin kasar Amurka da Chana, da yada jita jita da nufin yakar addinin musulunci da aiwatar da yakin tattalin arziki tsakanin Kasashan biyu.
Shiek Jingir yace cutar Corona karya ce, da ake nufin hana musulmi yin sallah da yin hajj a cewar sa idan bahaka ba, menene zai sa gwamnati ta huce akan zuwa masallaci
Shehun yayi kira ga masarautar saudia data bude manyan masallatai dake garin makka da madina domin musulmai su ringa ibadarsu.
“Akwai yancin addini a Najeriya kuma mutane basu zabi shugabanninsu ba da za su hanasu yan’cin addini. Inji shi
Ya kuma yi kira da cewa rufe makarantu babu abunda zai amfanar face jahilci, inda ya shawarci gwamnati da kada ta kulle makarantu.
Shiek Jingir ya ja hankalin yan jarida da su kiyaye wajan kawo rahoto akan cutar corona yana mai cewa hakan na jefa jama’a cikin tsoro.
A karshe ya gargadi musulmai da su kasance masu imani ga Allah wanda shikadai yake da ikon jarrabar bayinsa.
© Abubakar Saddiq
Post a Comment