Shahararren dan wasan Manchester United Paul Pogba ya kafa wata gidauniya don tara kudin yaki da cutar coronavirus.
Wannan cuta dai ta karade duniya, inda yanzu haka ta harbi mutane 167,000, tare da kashe dubu 6 da dari 5.
Annobar dai ta shafi harkar wasannin motsa jiki musamman kwallon kafa, inda a nahiyar Turai aka dakatar da dukkannin gasannin kwallon kafa, haka kuma aka dakatar da mahimman taruka dabam dabam.
Da yake bikin zagayowar ranar haihuwara a jiya Lahadi, inda ya cika shekaru 27, Pogba ya ce yana harin tara fam dubu 27 ne don taimakawa wajen yaki da shu’umar cutar.
Pogba ya ce, yana murnar kasancewa cikin koshin lafiya a daidai lokacin da wasu ke fama da rashin lafiya, saboda haka kamata ya yi y aba da tasa gudummawar wajen nema musu lafiya.
© hutudole
Post a Comment