Hukumomin Kasar Italiya sun ce, yau juma’a mutane 627 suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Coronavirus ko kuma COVID-19 abin da ya kawo adadin mutanen da suka mutu a kasar zuwa 4,032.
Alkaluman mutanen da suka kamu da cutar a Italiya sun zarce 47,000 sakamakon karuwar mutane kusan 6,000 a cikin sa’oi 24.
Kasar da ke dauke da mutane miliyan 60 yanzu ita ce kan gaba cikin jerin kasashen da wannan annuba tafi yi wa illa, yayin da China da ta samu nasarar dakile cutar ta koma ta biyu.
Matteo Bassetti, daraktan da ke kula da Ma’aikatar Yaki da Cutuka Masu Yaduwa ya ce, yanzu haka akwai mutane da dama da ke dauke da cutar kuma suna yada ta.
Gwamnatin Italiya na nazarin daukar matakin kara wa’adin zaman gida da rufe wuraren sana’oi fiye da ranar 25 ga wannan wata da aka bada umurnin a baya.
Shugabannin shiyoyin kasar da kuma Magadan-Gari sun bukaci gwamnati ta dauki karin matakai masu tsauri ciki har da hana mutane fita domin motsa jiki da rufe dukkan shaguna ranar Lahadi mai zuwa.
© hutudole
Post a Comment