Babban Limamin kasar Ghanar Shaikh Nuhu Sharubutu, ya karyata labarin da wasu kafafan sadarwa ta yanar gizo ke yadawa cewa malamin ya ce, ya halartawa musulmi su shagiya domin maganin cutar coronavirus.

 

Mai magana da yawun Shaihin malamin Shaikh Armaya’u Shu’aib ya shaida wa Aminiya cewa, malamin ya yi bayani ga al’ummar musulmin kasar Ghana da harshen Hausa cewa, suyi biyayya ga dokar da gwamnatin kasar ta kafa na hana taro a masallatai da coci-coci, inda ya nisance su cewa addini musulunci yana da cikakkun tanadi wajen matakin kariya ga cutar annoba.

 

“Bayan da Malam ya yi wannan bayani sai na fasara da turanci na rabawa wasu ‘yan jaridu, amma ko kadan babu maganar shangiya a cikin maganar da Imam na Ghana Shaikh Nuhu Sharubutu ya yi.” In ji shi.

Aminiya



© hutudole

Post a Comment

 
Top