A Najeriya yawan wadanda aka Gano na dauke da cutar sun kai 12. A jiya, Alhamis ne aka gano wasu karin mutane 4 a Legas dake dauke da cutar.
Saidai mutum na farko dan kasar Italiya da aka fara samu da cutar a Najeriya ya warke. Kamar yanda kwamishinan lafiya na jihar Legas, Akin Abayomi ya bayyanawa manema labarai.
Jihohin Najeriya da zuwa yanzu suka kulle makarantu saboda cutar Coronavirus/COVID-19:
Legas
Ogun
Kano
Benue
Anambra
Enugu
Naija
Babban birnin tarayya,Abuja.
Jihar Legas ta bayyana cewa tana bibiyar mutane 1300 da suka yi mu’amala da wadanda aka samu da cutar dan ganin an aunasu.
Uwargidan shugaban kasa, Hajiya A’isha Buhari ta kulle ofishinta na tsawon sati 2. Tace ta yi hakanne saboda wasu daga cikin ma’aikatanta sun dawo daga kasar Ingila inda tana daya daga cikin kasashen da Najeriya ta kullewa Boda.
A’isha Buhari ta kuma bayyana cewa diyarta data dawo daga kasar Ingila itama ta killace kanta na tsawon kwanaki 14.
Jam’iyyar Adawa ta PDP ta zargi shugaba Buhari da yin sakwa-Sakwa da lamarin cutar ta Coronavirus/COVID-19.
Kungiyar kwadago ta Najeriya tace maganar a rika cewa mutanen da suka shigo Najeriya daga kasashen dake dauke da cutar Coronavirus/COVID-19 su killace kansu bai kamata ba.
Shugaban kungiyar kwadagon,Ayuba Wabba ne ya bayyana haka inda yace, yawanci wanda suka shigo daga kasar wajene suka gogawa ‘yan Najeriya cutar.
Dan haka kamata yayi a rika killace su a guri na musamman saboda maganar a cewa mutum ya killace kanshi da kanshi a Najeriya ba zai yi aiki ba saboda lura da irin al’adunmu.
Hukumar yin rijistar katin dan kasa ta NIMC ta bayyana dakatar da aikin yiwa mutane rijistar sabods cutar Coronavirus.
An killace wanda suka yi mu’amala da dan kasar Amurkarnan da ake zargin ya kamu da cutar a Najeriya kuma ya mutu a jihar Ekiti.
© hutudole
Post a Comment