Bayan da majalisar dokoki ta jihar Kano ta dakatar da wasu ‘yan majalisar su biyar na tsawon watanni shida, ‘yan majalisar da abin ya shafa sun ce ba su koru ba.

 

Wasu masu nazarin kimiyyar siyasa sun ce a yi taka tsantsan wajen warware wannan matsala da ta kunno kai a zauren majalisar.

 

‘Yan majalisar da aka kora hutun dole na tsawon rabin shekarar sun hada da tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar Hon Labaran Abdul Madari da tsohon shugaban majalisar Hon Isyaku Ali Dan ja da Hon Garba Ya’u Gwarmai da Hon Mohammed Bello Butu-butu kana da Hon Salisu Maje Ahmed Gwangwazo.

 

A yayin zaman majalisar na jiya litinin, shugaban majalisar Hon Abdul’aziz Garba Gafasa ya ce majalisar ta dauki matakin ne saboda samun dakatattun ‘yan majalisar da laifin tada tunzuri da yamutsi a zauren majalisar a litinin din makon jiya.

 

Sai dai ‘yan majalisar guda biyar sun ce shugaban majalisar ba shi da hurumin jagorantar daukar matakin, kamar yadda guda daga cikin su Hon Labaran Abdul ya bayyana wa wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari.

 

“Za mu jira su fadi laifin da muka yi, ai dan majalisa ba wasa bane ba. Ni gaskiya ban dakatu ba, don ba a bi tsarin dokar da ya kamata a bi wajen dakatar da mu ba, kuma wannan lamarin ba zai hana ni shiga zauren majalisa ba,” a cewarsa.

 

Sai dai masanin kimiyar siyasa kuma malami a kwalejin share fagen shiga jami’a ta Kano Malam Kabiru Sa’idu Sufi ya ce ya dace ayi taka tsantsan wajen warware wannan takaddama.

 

Ya kuma kara da cewa “ya kamata a samar da maslaha ta fannin siyasa, saboda abin ya riga ya faru.”

 

Wannan dai shi ne karo na farko da majalisar dokokin Kano ta dakatar da ‘yayanta tun dawowar Najeriya tafarkin demokradiyya a shekarar 1999.

VOAhausa.



© hutudole

Post a Comment

 
Top