Alhaji Tanko Yakasai, shahrarran dan siyasa ne a Arewa dama kasa baki daya kuma daya daga cikin wadanda suka kirkiri Arewa Consultative Forum, a tattaunawar da Jaridar Punch tai dashi a ranar lahadi, ya bayyana dalilin da ya jawo tsige rawanin tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido a ranar 9 ga watan Maris din 2020.
Yakasai ya ce dalilin farko da yasa aka tsige rawanin sarkin shine yadda ya ke wa tsohon gwamnan Jihar Kano wanda ya nada shi sarki biyayya wato Kwankwaso. wanda kuma babu jituwa a tsakanin su da gwamnan da yake ci yanzu Abdullahi Ganduje.
Abu na biyu kuwa da ya jawo tsige tsohon sarkin shine rashin fahimtar tsohuwar al’adar jihar Kano wanda hakan yasa yake aiki ba tare da la’akari da ita ba,
“Ni haifaffan Kano ne kuma na san al’adun masarautar, Tun da nake yaro har zuwa yau, da sarki mai ilimi da mara ilimi basu magana da yawa. Suna mutunta kalamansu.
Shikuma tsohon sarki Sanusi an haifeshi a Kano ne amma tashin Legas ne da Kaduna. Mahaifinsa ma’aikacin gwamnati ne wanda ya kai matsayin babban sakatare.
Alhaji Yakasai ya kara da cewa, babban dan marigayi sarkin Kano, Ado Bayero ne yafi cancanta da karagar mulkin amma kuma gwamnan lokacin sai ya dora Sanusi.
A karshe ya bayyana cewa babban tushen matsalar ya faru ne bisa rashin fahimatar al’adar masarautar Jihar kano da tsohon sarkin ya gaza yin la’akari dasu wanda hakan ya faru ne bisa rashin tashin sa a Kano.
© Abubakar Saddiq
Post a Comment