Hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB ta bayyana cewa ta saki sakamakon jarabawar da aka rubuta ta 2020.
Hukumar ta bayyana cewa ta saki sakamakon jarabawar farko da dalibai suka rubuta ranar Asabar din data gabata, 14 ga watan Maris.
Jimullar sakamakon jarabawar da aka saki shine 312,000.
Ranar Lahadi ne aka saki sakamakon jarabawar kamar yanda JAMB ta bayyana. Ta kuma bukaci dalibai da su je su bincika sakamakon nasu.
Me hulda da kafafen watsa labarai na hukumar,Fabian Benjamin ne ya bayyanawa manema labarai da wannan lamari.
Inda yace suna fatan jarabawar ta wannan shekarar ta kasance an yi ta ba tare da matsala ba.
Koda a jiya, Litinin, 16 ga watan Maris, dalibai akalla 469,670 ne suka zauna jarabawar a gaba dayan kasarnan.
© hutudole
Post a Comment