Gwamnatin Tarayya ta haramtawa jami’anta da sauran ma’aikatanta fita kashashen waje, sakamakon barkewar cutar Coronavirus a fadin duniya wanda kungiyar lafiya ta duniya ta bayyana, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

 

Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Mista Boss Mustapha ne ya bayyana hakan a ranar Talata da daddare bayan kammala taron tattauna da Shugaban kasa kan hanyoyin da zaa shawo kan cutar ta CoronaVirus.



© hutudole

Post a Comment

 
Top