Ma fi akasarin mata na kasancewa cikin kunci da tunani mai tsanani game da abin da suke so sai dai wani lokacin kuncin yana samuwa ne ta hanyar kuntata wa zuciyarsu musamman wajen rashin yin dace ga abin da suke so.


Wasu matan sukan cusa wa zuciyarsu soyayyar wani namijin daban wanda bai ma san suna yi ba, wanda Hausawa ke cewa, “Son Maso Wani Koshin Wahala”. Kwarai kuwa haka ne babu ko shakka, domin kuwa bai san ma tana yi ba, ita kadai ta bar wa zuciyarta, sai kwana take tana wuni da shi a cikin zuciyarta.


Duk da dai ita soyayya Allah ke sa wa bawa cikin zuciya, ba tare da ya san so din zai shiga ba, kai ko da a ce ya shiga ma, wasu sukan yi kokarin kawar da son don gudun bacin rana ko kuma abin da ka je ya zo, wajen shi wanda suke so din ko don gudun wulakanci.
Kamar yanda maza suke shiga halin ha’ula’i yayin da suke son mace, ba tare da ta san suna yi ba, ko kuma su furta mata ta ki amince wa, haka wasu matan ma suke tsintar kansu a ciki wajen ingiza wa zuciyarsu son wanda bai san ma suna yi ba.

Sai dai a kan samu akasi yayin da mace ta zamo cikin wannan yanayi ta kasa fayyace wa wanda take so din soyayyarsa a gare ta don gudun kada ya dauke ta ba ta san me take ba, ko kuma ajinta ya zube matsayinta na ‘ya mace, karshe kuma ta bar wa zuciyarta har ta cutu.
Wata kuma tana iya sanarwa da shi wanda take so sakon zuciyarta ta kowace irin hanya ce, sai kuma shi namijin ya nuna ba ya sonta har ma ya samu hanyar da zai rinka wulakantata don kawai ta furta masa tana sonsa.

Ba ya la’akarin idan shi ne ya kasance hakan ya zai zama a gare ta? Sai dai ya rinka tunkaho yana fankamar wance ce take sonsa, shi ba ya sonta, ya shiga wulakanta ta, ta kowace hanya wanda inda shi ta yi wa hakan sai kowa ya ji labari a gari, wance na wulakanta wane ba ta kyauta ba.

Yin nazari da tunani yayin furta wa wanda yake sonka kalma mai dadin sauraro ko da kuwa kai ba ka sonsa na daya daga cikin abin da zai kara wa mutum daraja a idon masoyi ko masoyiyar, yi kokari ka faranta wa wadda take sonka ko da kuwa kai ba ka sonta wajen tausar zuciyarta, da kyawawan kalamai, ba kalaman da za su bakanta mata zuciya ba.

Kar dai ku manta masoya duk abin da Allah ya tsara babu tsumi, babu dabara, sai ya faru kuma Hausawa suka ce “Matar Mutum Kabarinsa”. Babu mai auren matar wani sai Allah ya kadarta daman can matarka ce, haka in macen ce ita ma, wanda Allah ya kaddara ya zamo mijinta babu yadda za ta yi, shi za ta aura.

A rage wulakanta masoyi ko masoyiya ko da kuwa ta furta maka da bakinta, ko kuma ta yi aike ga abokinka ko aminiyarta domin a sanar maka da son da take maka, tsananin so ke kawo hakan don wata zuciyar na iya jure wa, wata kuma zuciyar ba ta iya jure wa har sai ta furta za ta iya samun sauki.

Soyayya na iya jefa masoyi ko masoyiya halin da ba a iya tunanin fada wa, haka ma wata kunyar takan iya raguwa yayin da zuciya ta harbu ga wanda take so, tsananin soyayyar sai ta janye kunyar ta matsar gefe guda a sanarwa da juna.

Kalamai masu dadi na iya sa wa ko da namijin ba shi da burin auren macen daga baya in Allah ya kadarta matarsa ce sai ya ji soyayyarta ta fara ratsa cikin zuciyarsa. A lokacin ne zai je ba tare da jin wata kunya ba, tunda daman ba wulakanta ta ya yi ba. Sabanin inda wulakanta ya yi daga baya ya dawo ya ji soyayyarta a zuciya ba zai iya koma wa ya tunkare ta ba, sai dai ya tura waninsa walau aboki ko kuma kawarta don shawo masa kanta.

Hirar Masoya Cikin Kalaman Soyayya Son Maso Wani:

• Zuwa gare ka ya ma’abocin hasken idaniyata, hakika zuciyata ta kamu da tsantsar kaunarka burina kawai ka amince min in zamo abokiyar tarayya a gare ka.

• Sai dai kash! Ga shi kuma kin makara, babu soyayya a tare da zuciyata.

• Ka taimaka wa marainiyar zuciya hakika rashinka zai zama tamkar barazana ga rayuwata.

• Ki yi hakuri ki rabu da ni ba na son na sake fada wa tarkon da dakyar na fita daga cikinsa.

• Kada ka juyan baya ka zamo mai karbar kokan barata na yi alkawari zan ruke maka alkawari ba zan kautar da zuciyar ka ba.

• A baya an gaya min abin da ya fi haka wanda kash! Sai da na zo ina kuka da idaniyata.

• “Trust me my heart beat” ba na son ka kasa yadda da kaddara ina so ka sani, ba duka aka taru aka zama daya ba.

• Ki yi hakuri gaskiya yanzu ba na jin zan iya soyayya nakan ji bacin raina idan aka kira wo kalmar soyayya don haka nake cewa ki fita harkata.

• Ba zan iya ba, ba zan iya ba, ba zan iya ba, kana so na rasa rayuwata ke nan? Duk ran da ka ga na rabu da kai hakika na bar taka doran duniya na koma ga mahaliccina.

• Dolenki kuwa ki hakura da ni domin kuwa soyayya, na yi abin da ke ba ki yi ba, ke fa mace ce kuma na tsani soyayya ne dalilin ku mata, ta ya za a yi na yarda da ke? Soyayya ta yi min tabon da ba zai taba warke wa a cikin zuciyata ba.

• Gaskiya kana ba ni mamaki kana magana kamar wanda ka manta cewa halayyar mutane daban-daban Allah ya yi musu. Ina so ka sa a ranka cewa Allah ya jarabce ka a karon farko amma insha Allahu za ka ji dadin soyayya da ni.

• Amma abin da nake so da ke shi ne, ina so ki bar ni na yi tunani nan da kwana uku ko hudu.

• Idan har ka yarda da ni na yi maka alkawarin zan rike amanarka, ba zan taba yi maka kishiya ba, kai ne daya tilo babu wani.

Tambayar Yau Tana Cewa

Idan mace ta furta maka kalmar so, ya za ka kasance a wannan lokacin, kuma wace irin amsa za ka ba ta? Yi bayani a takaice. 

Idan kika ga namijin da kike so, shin za ki iya furta masa cewa kina sonsa ko kuwa za ki hakuri ki kyale? Fadi hanyar da za ki bi don magance wannan matsala.
Sai na ji daga gare ku.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top