Innalillahi wa inna ilaihi raji’un

 

Wata matashiya da bata samu makin da take so ba a jarabawar share fagen shiga jami’a ta JAMB ta kashe kanta.

 

Matashiyar mai suna Zainab ta hallaka kantane bayan data ga sakamakon da bashi take tsammani ba.

 

Rahotannin dake yawo a kafafen sada zumunta sun bayyana cewa Zainab na kan hanyartane na zuwa Asibiti inda zata kaiwa ‘yar uwarta da ke Nakuda abinci.

 

A nanne ta duba Sakamakon jarabawarta wanda bai mata daidaiba. Ta nufi Kyamis inda ta sayi Sniper ta je masallaci ta yi addu’a sannan ta sha.

 

Wani ya ganta sanda take kakarin mutuwa aka garzaya da ita Asibiti amma duk da haka sai da ta mutu.

 

Muna fatan Allah ya jikanta.

 

 



© hutudole

Post a Comment

 
Top