COVID19 yayi dai dai da yakin duniya na uku inji ministan ayyuka da gaidaje Fashola.

Ministan wanda yayi jawabi a lokacin da yake duba ayyuka a garin fatakwal.

Ya kamanata cutar Corona a matsayin yakin duniya na uku wanda akan iya yaki da itane ta hanyar jami’an lafiya, magun guna da kuma bincike.

Tun bayan bullar cutar COVID19 a Najeriya hukumomi Ke kokari wajan an dakile kara ya duwar cutar a fadin kasa baki daya koda gwamnatocin jihohi sun yi wannan hubbasa wajan ganin an rufe makarantu domin Kara dakile ya duwar cutar wanda ya hada da dakatar da tarukan jama’a.

Har dai zuwa yanzu ma’iya cewa cutar Corona da aka fi sani da COVID19 ta zamewa duniya alakakai, wanda harzuwa yanzu ba a shawo kanta ba, sai dai ma’iya cewa ana samun cigaba wajan dakile kara ya duwarta a fadin duniya baki daya.



© Abubakar Saddiq

Post a Comment

 
Top