Shugaban jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, Adams Oshiomhole ya ce, ya gane kuskurensa dangane da rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar ya kuma kusa raba shi da mukaminsa, kuma yanzu haka a shirye yake ya yi aiki da sauran shugabannin jam’iyyar a cewarsa.

 

Yayin da yake jawabi bayan ya koma ofishinsa sakamakon umurnin kotun daukaka kara na jingine hukuncin wata kotun tarayya, Oshiomhole ya ce an tilasta masa ya amince da cewa, ba shi ne shugaban da ya fi kowa kwarewa ba, amma kuma babu wanda bai amince da jajircewarsa ba.

 

Shugaban ya ce, ya fahimci muhimmancin sasantawa da jama’a kan yadda yake gudanar da mulkinsa domin ganin an fahimci juna wajen yin aki tare.

 

An dai samu rarrabuwar kawuna ne tsakanin masu goyan bayan shugaban da masu adawa da shi sakamakon dakatar da shi da mazabar sa ta yi, abin da ya sa wasu shugabannin jam’iyyar rugawa kotu domin ganin ya bar kujerarsa.

 

Kafin dai wannan, Oshiomhole ya yi ta takun saka da wasu shugabannin Jam’iyyar abin da ya sa aka dakatar da su daga kujerar su.

 

Oshiomhole ya zargi wasu gwamnoni da masu neman takarar shugaban kasa a shekarar 2023 a matsayin masu neman ganin bayansa, yayin da jagoran Jam’iyyar Bola Ahmed Tinubu da wasu gwamnoni suka fito karara suka goya masa baya.

 

Sanya bakin Tinubu da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hana gudanar da taron shugabannin Jam’iyyar na kasa wanda aka shirya amfani da shi wajen korar shugaban jam’iyyar.



© hutudole

Post a Comment

 
Top