Rahotanni daga kasar Paraguay sun ce jami’an tsaron kasar sun saki tsohon dan kwallon Brazil Ronaldhinho bayan sun kama shi da laifin shiga kasar da fasfo na jabu.
Ronaldinho ya shiga Paraguay ne tare da dan uwansa da kuma Manajansa Roberto Assis da fasfo na jabu da hakan ya saba wa dokar shiga kasar.
Idan ba a manta ba a shekarar 2018 ne Brazil ta kwace fasfo din Ronaldhinho saboda aikata wani laifi da hakan ya sa dan kwallon yake amfani da fasfo na jabu don shiga wasu kasashen duniya ba bisa ka’ida ba.
Rahoton ya ce jami’in da ke tuhumar Ronaldhino da shiga Paraguay ba bisa ka’ida ba Federico Delfino ya tabbatar da sakin tsohon dan kwallon da ayarinsa a lokacin da yake hira da manema labarai. Ya ce tuni mahukunta kasar suke gudanar da bincike don gano yadda tsohon dan kwallon da ayarinsa suka mallaki fasfo na jabu.
Ronaldhinho wanda ake yi wa lakabi da Gaucho ya taba yi wa kulob din FC Barcelona na Spain da AC Milan na Italiya kwallo. Ya samu nasarori a fagen kwallon kafa ciki har da zama Gwarzon Dan Kwallon Kafa na duniya. Ya taba lashe wa kasarsa Brazil kofin kwallon kafa na duniya a 2002.
© hutudole
Post a Comment