Wata kungiyar gamayyar masu rike da masarautun gargajiya na jihar Ekiti da ake kira da suna Mogajis ta bayyana cewa zata kaiwa tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ziyarar nuna goyon baya.
Kungiyar ta kuma caccaki gwamnan jihar ta Ekiti, Kayode Fayemi wanda shima dangantakarshi da Sarakunan gargajiya a jihar ta fara tsami.
Ta bayyana cewa ya kamata gwamnan ya tunafa akwai lokacin da zai sauka daga mukaminsa sannan wadannan sarakuna sun yiwa jama’a aiki, kamata yayi ace ana girmamasu bawai wulakantasu ba.
Sun kuma jawo hankalin gwamnan Kano,Dr. Abdullahi Umar Ganduje da cewa ya kula fa idan shine yau ba shine gobeba.
© hutudole
Post a Comment