Shugaban kungiyar Izala ta JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce ya kamata gwamnatin Najeriya ta dauki duk matakan da su ka zama wajibi kamar sauran kasashen duniya wajen rigakafin cutar coronavirus, ko da matakan sun hada da dakatar da zirga-zirgar da ba ta zama wajibi ba da kuma kula da yadda jama’a ke cudanya.

 

Malamin ya kuma bukaci Musulmai su kyautata dabi’un su da guje wa duk abinda zai kai su ga sabon Allah, don kuwa sabon Allah kan kawo annoba. Bayan haka Sheikh ya bukaci gudanar da addu’o’i na musamman na Alkunut don neman taimakon Allah ya kawo karshen wannan annoba.

 

Malamin ya ce idan a ka samu bullar annoba a wuri, bai kamata mutane su nufi inda annobar ta ke ba, sannan wadanda ta riska a gida su dakata a nan su nemi magani don gudun yada cutar ga wadanda ke da lafiya.

 

Sheikh Bala Lau ya yi addu’ar Allah ya kawo karshen wannan cuta don jama’a su samu damar ci gaba da Umrah da kuma zuwa aikin Hajjin bana da za a fara a ranar 28 ga watan Yuli.

 

Ita ma babbar kungiyar darikar Tijjaniyya Ansarul Din Al-Tijjaniyya ta bukaci duk ‘yan darikar su zauna a gida su yi addu’a bayan dage taron Maulidin Shehu Ibrahim Niasse. Sakataren kungiyar na kasa Alkassim Yawuri ne ya fitar da sanarwar bayan wani taron gaggawa na kungiyar da aka yi a Abuja.

 

Akalla dai an kafe takardun sakonni a ma’aikatun gwamnati da ke shawartar mutane su ankarar da jami’an lafiya da zarar sun ga mai alamun cutar coronavirus.



© hutudole

Post a Comment

 
Top