Memba mai wakiltar mazabar Gombi a majalisar dokokin jihar Adamawa, Hon. Japheth Kefas, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta hanzarta daukar karin jami’an tsaro don kawo karshen hare-haren kungiyar Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas.

Dan majalisar wanda shine mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar ya zantane da wakilin Blueprint a ofishinsa dake Yola jihar Adamawa.

Ya danganta hare-haren da yan Boko Haram ke kaiwa da kuma nasarorin da suka samu kan al’umma, musamman a yankin Arewa masu gabas nada nasaba da rashin isassun jami’an tsaro da kuma rashin tattara bayanan sirri da kuma karancin ma kamai, a cewar sa idan aka kwatanta dana masu tada zaune tsaye.

Ya kara dacewa “lalle babu isassun jami’ai domin a kauye na zakaga Jami’an yansand biyu ne taya zasu iya fafatawa da yan tada kayar baya da suke zuwa dayawan su.

Dan majalisar yayi Kira da gwamnati data yi wani abu ta hanyar kara daukan Jami’an tsaro ta yadda ko wanne kauye a cikin kananan hukomomi bakwai da ke fama da hare-haran yan Boko Haram zasu samu Jami’ai guda 50.



© Abubakar Saddiq

Post a Comment

 
Top