A karon farko a birnin Washington na Amurka za a gwada allurar riga-kafin cutar Corona da aka samar a kasar.
Kamfanin dillancin labarai na AP dake Amurka ya rawaito wasu jami’an gwamnatin kasar na cewa, za a gudanar da gwaji riga-kafin a Cibiyar Binciken Lafiya ta Permanente Kaiser dake Seattle inda aka tara kudin yin maganin.
Mahukunta sun ce za a yi gwajin a kan mutane 45 masu lafiya, kuma maganin ba zai janyo su kamu da cutar ba, kawai za a ga irin tasirin da yake da shi.
Mahukuntan sun ce za a dauki tsawon watanni 8 zuwa shekara 1 kafin a kammala samar da maganin cutar Corona.
Alokacinda Corona ke ci gaba da yaduwa, kasar ta fara kokarin samar da maganinta.
Alkaluman Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya sun ce kusan mutane dubu 160 Corona ta kama a duniya baki daya.
Covid-19 da ta faro daga garin WUhan na China ta kuma yi ajalin mutane dubu 5,800.
© hutudole
Post a Comment