Dan wasan tsakiya na faransa da kuma Juventus Blaise Matuidi na dauke da cutar coronavirus.

 

A shafin yan kungiyar tasu na yanar gizo sun ce, an yima Matuidi gwaje-gwaje kuma hakan ne ya tabbatar da cewa yana dauke da cutar Covid-19. Kuma a ranar laraba 11 ga watan maris dan wasan ta taimaka wurin killace kanshi a gida.
Za a cigaba da kula da shi kuma zai bi dokar da gwamnati da hukumar lafiya suka tsara gami da cutar, babu wata alamar cutar a tattare da shi a halin yanzu. Kuma ya kasance dan wasa na biyu daya ya fara kamuwa da cutar Covid-19 a Juventus bayan dan wasan baya su Daniele Rugani.
A ranar 11 ga watan maris ne Rugani ya fara killace kanshi ayayin da kulob din Serie A suke dubo sauran mutanen daya yi mu’amala dasu.


© hutudole

Post a Comment

 
Top