Kotun daukaka kara dake babban birnin tarayya,Abuja a Ranar Litinin,16 ga watan Maris ta mayar da Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam’iyyar APC inda ta yi watsi da hukuncin babbar kotun gwamnatin tarayya na dakatar dashi.

 

Kotun karkashin jagorancin mai shari’a Abubakar Datti Yahaya na alkalai 3 ne ya bayyana haka . Ya jawo hankulan jam’iyyu da su rika kokarin warware matalolinsu a cikin gida maimakon damun kotu.

 

Jim kadan bayan mayar dashi shugaban jam’iyyar,Adams Oshiomhole ya kira taron gaggawa na kwamitin gudanarwa na jam’iyyar da za’a yi a yau, Talata, 17 ga watan Maris a sakatariyar jam’iyyar dake Abuja da misslin karfe 12.

 

Me hulda da jama’a na jam’iyyar Lanre Issa-Onilu ne ya bayyanawa manema labarai haka inda yace ana bukatar duk wadanda ke cikin kwamitin su halarci taron dan za’a tattauna muhimman batutuwa.

 

 



© hutudole

Post a Comment

Emoticon
:) :)) ;(( :-) =)) ;( ;-( :d :-d @-) :p :o :>) (o) [-( :-? (p) :-s (m) 8-) :-t :-b b-( :-# =p~ $-) (b) (f) x-) (k) (h) (c) cheer
Click to see the code!
To insert emoticon you must added at least one space before the code.

 
Top