Sanarwa daga mahukuntan kasar Saudiyya ta bayyana cewa an kulle manyan masallatai biyu na Harami dana Annabi S.A.W.

 

Me magana da yawun fadar gwamnatin Saudiyya,Hani Bin Hosni Haider ya bayyana haka inda yace daga Yau Juma’a ne za’a hana mutane shiga masallacin dan Ibada, kamar yanda kamfanin dillancin labaran kasar,SPA ya ruwaito.

 

A baya dai an hana Sallolin jam’i a sauran masallatan kasar banda manyan masallatan biyu amma daga baya suma gashi an Rufesu.

 



© hutudole

Post a Comment

 
Top