Shin kasan dalilin da yasa ake kiran Corona da Covid-19 ?

Hukumar lafiya wadda aka fi sani da WHO ita ce ta samar da sunan a ta bakin shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus wanda ya shai dawa manema labarai, akan dalilin su na samar da sunan Covid-19 a madadin Corona.

A cewar Hukumar ta Samar da sunan ne domin yawan mutanan da cutar ta hallaka da kuma kawar da kyama ga masu dauke da cutar.

Cutar corona ta farane daga kasar chana wanda a hankali ta fara bazuwa har zuwa kasashan duniya.

Yadda aka samar da Covid-19 shine

“Co” an samo shine daga farkon cutar Co-rona, “vi” shi kuma yana nufin Virus “d” yana nufin Disease sannan 19″ an sanya ta ne domin a shekarar cutar ta fara bulla.

Ita dai cutar corona kwayoyin cututtuka ne da suke kama numfashi, wanda asalin cututtukan sun samu ne daga dabbobi jinsin tsin-tsaye da sauransu.



© Abubakar Saddiq

Post a Comment

 
Top