An samu labari daga ESPN cewa dan wasan gaba na Paris saint German Neymar ya bar kasar Faransa tare da Tiago Silva sun koma kasar su ta asali wato Brazil saboda annobar cutar Covid-19.

PSG ta baiwa gabadaya yan wasan ta damar barin kasar ta faransa tun kafin a  kulle ta kuma tace su killace kansu a duk inda zasu je ko kuma su tsaya a Paris.
Dan wasan bayan su Marquinhos wanda ya kasance dan Brazil ne shi amma ya zabi daya cigaba da zama a kasar faransan.
Kocinan PSG sun umurci yan wasan da cigaba da motsa jikin su kamar yadda suka saba.


© Ahmad A

Post a Comment

 
Top